Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Jama’a su Ci Gaba da Hurda da Bankuna


Babban bankin Najeriya (CBN) ya kamala bitar masu hurda da bankuna.

Babban bankin Najeriya (CBN) ya kamala bitar masu hurda da bankuna a Najeriya ta yanda zasu san hakokin su agarin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Hajiya Khadija Kasim daraktan mai kula da sashen ilimantar da jama’a akan hakkokin su da kare su ta babban bankin Najeriya, tace kare hakokin jama’a,masammam na masu hurda da bankuna,abune da dama jama’a ke jira.

Tace tayi na’am da yanda jama’a suke fitowa suka sauraren su a duk inda suka je a fadin kasar,suna kuma rungumar shawarwarin da ake basu.

Daraktan,tace ya kamata jama’a su ci gaba da hurda da bankuna domin zasu ci gaba da fito da shirin da ban da ban domin ilmatar da jama’a.

Ta kuma shawarci jama’a da su guji masu zawarcisu nasu kawo ajiyar kudi dayi masu karyan ruwa mai yawa.
Ya Kamata Jama’a su Ci Gaba da Hurda da Bankuna - 3'22"
XS
SM
MD
LG