Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yiwu Mu Ladabtar da Lauyan Kwankwaso-NBA


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Kungiyar lauyoyi ta kasa a Najeriya tace zata ladabtar da lauyan tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso idan yar korafin da kotu tayi ya tabbata.

Kungiyar lauyoyi ta najeriya reshen jihar Kano tace zata dauki matakan ladaftarwa akan lauyan tsahon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso Barrister Okechukwu Nweaze sakamakon nuna dabi’ar wuce gona da iri a gaban kotu.

Sai dai kotun tace duk wani mataki da zata dauka ya dogara ne da hujjar data samu daga kotun.

Babbar kotun Kano ce ta yanke hukumcin cewa, kungiyar ta ladabtar da lauyan saboda shishshigin da ya nuna a gabanta yayinda yake kokarin kare tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso game da karar da aka ce tsohon gwamnan ya shigar, yana neman kotun ta dakatar da duk wani yunkuri da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC zata yi na kama shi, biyo bayan korafin da kungiyar ‘yan fensho ta jihar Kano ta gabatarwa EFCC cewa, tsohon gwamnan yayi rubda da ciki da biliyoyin naira mallakar ‘yan fansho.

Yayinda yake kokarin kare tsohon gwamnan a gaban kotun, Barrister Okechukwu Nweaze, ya nemi kotun ta hana EFCC wancan yunkuri nata na kama tsohon gwamnan, yana mai cewa, hukumar na kokarin keta alfarmar tsohon gwamnan a matsayin na dan majalisar dattawan Najeriya.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko daga Kano

Rahoton Mahmud Ibrahim Kwari-2:31"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG