Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yiwu Sinadarin Bitamin D ya Taimakawa Masu Ciwon Makyarkyara


Bitamin D
Bitamin D
Wani karamin bincike da aka gudanar a kasar Japan na nuni da cewa, mai yiwuwa ne sinadarin bitamin D ya taimakawa wadansu masu wani nau’in halitta dake fama da cutar makyarkyara.

An gundanar da binciken ne a a kan mutane 114 dake fama da cutar inda aka ba wadansu kwayar maganin bitamin D, yayinda aka ba wadansu wani maganin dabam na tsawon shekara daya, bayan da aka gwada su sai aka tarar da yanayin wadanda suke da wani irin nau’in halitta bai kara muni ba, kamar yadda na wadanda suka sha wani magani ya yi.

Bincike da aka gudanar a baya ya nuna cewa mutane da suke fama da cutar makyarkyara basu da isasshen sinadarin bitamin D a jininsu ko da yake ba a iya tantance ko rashin sinadarin ne yake sa kamuwa da cutar ba.

Jikin mutum yana samun sinadarin bitamin D daga hasken rana yana kuma taimakonshi wajen samun sinadarin kara karfin kashi.

Sai dai likitocin dake gudanar da wannan binciken sunce ana bukatar kara nazari da bincike sosai kafin a amince da ba dukan masu ciwon makyarkyara maganin bitamin D.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG