Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahajjata: Saudiyya Ta Wajabta Nuna Shaidar Rigakafi


Hukumar lafiya a Saudiyya ta kawo sabon tsari bana da ya sanya ya zama wajibi maniyyata su nuna shaidar rigakafi na cutar shan inna da agana daga duk alhazan da su ka fito daga kasashen da a ke samun irin wannan ciwo.

Tsarin dai ya biyo bayan sabbin matakai ne na lafiya daga hukumar lafiya ta duniya “WHO”. A baya dai alhazan kan tafi da katin shaidar rigakafi na cutukan da kan ratsa kan iyaka da a ke kira Yalon Kati ko “Yellow Card” a turance da a kan cusa a cikin Fasfo din alhazan.

A takardar manema labaru daga jami’ar labarun hukumar alhazan Najeriya NAHCON, Hajiya Fatima Usara, ma’aikatar lafiyar ta Saudiyya ta kuma shawarci alhazai da su kaucewa haduwa kai tsaye da dabbobi musamman rakuma da kuma mutanen da ke da wata cuta mai iya yaduwa.

Jagoran likitan alhazan Dakta Ibrahim Kana ya yi karin bayanin cewa rakuman na dauke da zazzabin gabar ta tsakiya da a ke kira Corona virus.

Wanda hakan ya sanya ba da shawarar amfani da kariyar hanci a wajen zirga-zirga da zai rage fargabar yaduwar wata cuta daga atishawa ko tari.

Sannan ga kasashe masu zazzabin ZIKA da wani sauro ke haddasawa, an bukace su, su kaucewa duk yanayin da za su gamu da sauron.

Saudiyya na bukatar duk maniyyaci ya samu rigakafi daga mura mai zafi kwana 10 gabanin tafiya aikin hajjin.

An ba da wani umurnin fesa magani ga duk hanyoyin da alhazai daga kasashe masu wata cuta za su bi wato wannan ya nuna daukar matakan fesa maganin a wa imma a jirgi ko motocin da za su yi jigilar alhazan don inganta hanyoyin kiwon lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG