Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Bude Filayen Jiragen Sama a Najeriya


Wani jirgi a birnin Landan

An soma hada-hadar sufurin jiragen sama a Najeriya tun bayan bullar cutar Covid-19 a watan Maris da ya tilasta tsayar da harkokin zirga-zirgar jirage a kasar baki daya.

Sai dai hakan ya biyo bayan shimfida wasu ka’idojin kariya daga kamuwa da cutar wanda cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar NCDC ta fitar da kuma hukumar sufurin jirage ta kasar.

Daya daga cikin jiragen da suka sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa wato Nmandi Azikwe Int'l Airport dake babban birnin tarayyar kasar Abuja, daga Legas ya taso.

Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe a ranar da aka bude filin jiragen.
Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe a ranar da aka bude filin jiragen.

Yanzu jihohi biyu ne gwamnatin kasar ta ba da umarnin filayen jiragensu su soma aiki daga ranar 8 ga watan Yuli, tun bayan sama da watanni uku da aka dakatar da duk wata zirga zirga da ta shafi jiragen.

A cewar Kyaftin Rabiu Yadudu da ke zama babban shugaban hukumar filin jirgin sama ta Najeriya, "an dauki matakai da dama kuma an bai wa ma’aikata da ke wajen horo na musamman kana a shirye suke don tabbatar da an kare lafiyar al’umma."

Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe a ranar da aka bude filin jiragen.
Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe a ranar da aka bude filin jiragen.

A ranar 11 ga wannan wata na Yuli ake sa ran filin jirgin sama na Malam Aminu kano dake jihar Kano da na Port Harcourt da Owerri hada da Maiduguri za su soma aiki yayin da a ranar 15 ga watan sauran filayen jiragen sama a sauran jihohin kasar suma za su soma aiki.

Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe a ranar da aka bude filin jiragen.
Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe a ranar da aka bude filin jiragen.

Idan za a tuna tun a watan Maris gwamantin Najeriya ta ayyana dakatar da dukkan hada-hadar sufurin jiragen sama sakamakon bullar cutar coronavirus a kasar, wanda ya zuwa yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar ya haura dubu 29,789 ya kuma yi sanadin mutuwar mutane 667 kana mutane 12,108 sun warke daga cutar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG