Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Yadda Aka Rantsar Da Sabon Shugaba a Burundi


Evariste Ndayishimiye, sabon shugaban kasar Burundi

A yau Alhamis aka rantsar da sabon shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye a filin wasa na Ingoma da ke birnin Gitegay, mako daya bayan mutuwar shugaba mai barin gado Pierre Nkurunziza ya yi.

An shirya rantsar da Ndayashimiye a watan Agusta amma Kotun Tsarin Mulki ta bada umurnin a rantsar da shi ba tare da bata locaci ba bayan mutuwar Shugaba mai barin gadon.

Ndayashimiye ya zamo sabon shugaban Burundi ne yayin da ya samu kuri’u kaso 68 cikin 100 a zaben na watan Mayu wanda ya hana jam’iyyar adawa cika burinsu na ganin an soke zaben bisa zargin magudi.

Jam’iyyar CNDD-FDD ce ta zabi Ndayashimiye da ya gaji Nkurunziza kuma zai yi wa’adin shekara bakwai kafin sake tsayawa a zabe shi.

Daga cikin kalubale na farko da zai fuskanta shi ne rage yaduwar cutar coronavirus. Ko a wurin rantsar da shi, an bukaci jama’a da su fita da wuri domin a sami gwada zafin jikinsu.

Ya zuwa yanzu, Burundi na da wadanda aka tabbatar suna dauke da COVID-19 mutun sama da 100 kuma mutun daya ne yam utu da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG