Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Tarbi Ronaldo A Iran


Dandazon Iraniyawa da suka tarbi Ronaldo a lokacin da kungiyarsu ta Al Nassr ta sauka a Tehran (Hoto:X /Twitter/Al Nassr)
Dandazon Iraniyawa da suka tarbi Ronaldo a lokacin da kungiyarsu ta Al Nassr ta sauka a Tehran (Hoto:X /Twitter/Al Nassr)

An ji mutanen da suka yi dandazo a babban zauren otel din Espinas Palace, suna ta ambaton sunan Ronaldo.

Daruruwan masoya kwallon kafa a Iran, sun yi tururuwar zuwa wani otel don kallon fitaccen dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo yayin da kungiyarsa ta Al Nassra ta isa Tehran babban birnin kasar a ranar Litinin.

An ji mutanen da suka yi dandazo a babban zauren otel din Espinas Palace, suna ta ambaton sunan Ronaldo.

Ronaldo a Iran (AP)
Ronaldo a Iran (AP)

Masoya kwallon kafar da suka hada da yara da manya, sun yi ta kutsa kai cikin ‘yan sandan da ke tsaron otel din.

Wannan ita ce ziyarar farko da Ronaldo ya kai kasar ta Iran da Al Nassr wacce za ta fafata da kungiyar Persepolis ta kasar Iran a yau Talata a gasar Zakarun Nahiyar Asiya ta AFC.

A farkon shekarar nan Iran da Saudiyya suka maido da huldarsu ta diflamasiyya bayan wani shiga tsakani da China ta yi.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG