Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Najeriya

Yadda Ake Tauye Hakkokin Miliyoyin Yara a Najeriya


Wasu yara a kasar Afirka ta kudu
Wasu yara a kasar Afirka ta kudu

Masana sun kiyasta cewa yara sama da miliyan 30 a yankin kudu da hamadar Sahara ba sa zuwa makaranta, kuma kashi 54 cikin 100 na yaran mata ne, lamarin da ya fi tsananta a Najeriya.

Galibin yara ‘yan Afirka na fuskantar tarin matsaloli na zamantakewa musamman a yanayin kasa kamar Najeriya da ke fama da talauci, durkushewar tallalin arziki, rikicin yan bindiga dadi, mayakan Boko Haram, rikicin siyasa, wanda hakan ka iya tauye wa yaran hakkokinsu.

Tauye hakkin yara bai tsaya ga cin zarafin su a lokuta irin na yaki ba, a wasu yankunan nahiyar Afirka, ana yawan samun ayyuka da ke nuna yadda ake cin zarafin yara a rayuwarsu ta yau da kullum, wadanda su ka hada da fataucin yaran, sa su aikin da ya fi karfinsu, yi musu auren wuri da yin lalata da su da kuma rashin ba su ingantaccen ilimi.

Wasu yara a kasar Zimbabwe wadanda wata kungiya ke biya wa kudin makaranta
Wasu yara a kasar Zimbabwe wadanda wata kungiya ke biya wa kudin makaranta

Hajiya Sadiya Tahir, shugabar wata kungiya da ke sa ido akan kanana yara da mata a jihar Filato mai suna ‘’Muma Mata ne’’ ta ce "yawan haihuwan da ya wuce kima na cikin abubuwan da ke janyo rashin baiwa yara hakkinsu yadda ya kamata."

"Mu iyaye mata ya kamata mu sanya ido mu rage yawan haihuwa, saboda mu iya kula da yaran da ke gabanku."

A cikin kwanakin nan an dauki wani sabon salo na cin zarafin yara da yi musu fyade, lamarin da ke neman zama ruwan dare a kasar.

Malama latifa Hussain shugabar mata ta unguwar Efab dake Lifecamp a Abuja ta ce "rashin wadatar zuci da ilimi su ke kan gaba a aukuwar ire iren wannan masifu acikin al’umma."

Matar Shugaban Amurka, Melania Trump a lokacin da ta ziyraci wata makaranta a kasar Malawi inda ake koya wa yara karatu a waje
Matar Shugaban Amurka, Melania Trump a lokacin da ta ziyraci wata makaranta a kasar Malawi inda ake koya wa yara karatu a waje

A cikin shekarar 2003, Nigeria ta amince da dokar kare hakkin kananan yara wanda zai yi duba da kuma mutunta sharrudan dokoki da aka shimfida da zai kare su, sai dai ya zuwa yanzu jihohi 21 ne kadai cikin 36 har da babban birnin tarayyar kasar su ka kaddamar da wannan doka.

Wani rahoton bincike na duniya kan rayuwar yara, ya bayyana cewa, ana cin zarafin daya daga cikin yara hudu a duk fadin duniya, wajen sanya tsaiko a lokutan da ya kamata su yi amfani da shi don samun ilimi, girma da kuma walwala tsakanin ‘yan ’uwansu yara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG