Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Bama-bamai Suka Tashi a Maiduguri


Nigeria Violence

Rundunar 'yan sandan jihar Borno, Mista Damian Chukwu ya tabbatar da tashin wasu bama-bamai a garin Maiduguri da ake tunanin wasu mata ne suka shiga garin da su.

Kwamishanan 'yan sandan jihar ya fitar da wata sanarwa inda ya ce tashin bama-baman ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida da suka hada da 'yan kunar bakin waken hudu.

Mista Damian ya kuma ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 1:30 na dare lokacin da 'yan kunar bakin waken suka shiga ta wani kauyen Alkomi dake kan hanyar zuwa garejin Muna.

Kwamishanan ya ce an yi dace mutanen anguwar sun gansu kuma sun taka masu birki.

Amma yayin da mutanen anguwar ke kokarin hana su sai matan suka soma tayar da bamabaman daya bayan daya suka kashe kawunansu tare da wasu mutane biyu.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:43 0:00

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG