Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Bishiya Ta Halaka Wata Mata a Mozambique

Yadda guguwar Kenneth ta yi kacakaca da wani gida a Mozambique a wannan hoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu daga kafafen sada zumunta na (SolidarMed)
Yadda guguwar Kenneth ta yi kacakaca da wani gida a Mozambique a wannan hoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu daga kafafen sada zumunta na (SolidarMed)

Hukumomin kasar ta Mozambique sun ce, mutum dayan da ya rasu, wata mata ce da bishiya ta fada a kanta, a birnin da ake kira Pemba.

Muhaukaciyar guguwa ta biyu da ta abkawa kasar Mozambique cikin makonnin shida, ta halaka mutum guda.

Guguwar har ila yau, ta lallata gidaje da dama tare da tunbuke turakun wutar lantarki a cewar hukumomin kasar.

Guguwar wacce aka wa lakabi da Kenneth, ta sauka ne da yammcin Alhamis a arewacin kasar, tana tafe da iska mai gudun kilomita 220 cikin sa’a guda, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yi hanzarin fitar da gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa.

Hukumomin kasar ta Mozambique sun ce, mutum dayan da ya rasu, wata mata ce da bishiya ta fada a kanta, a birnin da ake kira Pemba.

A 'yan makwanni da suka gabata, guguwar Idai ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a yankin kudancin Afirka, cikin har da kasar Mozambique.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG