Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Gobara Ta Yi Barna a Mujami'ar Notre Dame Mai Dadadden Tarihi


Lokacin da jami'an kashe gobara suke kokain shawo kan gobara a Mujami'ar Notre Dame Cathedral a birnin Paris, Faransa, Afrilun 15, 2019.

Wutar, wadda a wani lokaci sai da ta yi sama da tsawon mita 10, ta lalata akasarin rufin majami’ar inda har hasumiyar rufin ta fadi.

Gobara ta yi barna mai matukar yawa ga sananniyar majami’ar nan ta Notre Dame Chathedral da ke birnin Paris.

Amma ‘yan kwana-kwana sun ce sun kare hasumiyoyi biyu na ginin, da kuma wani ginin dutse.

Shugaban hukumar kashe gobara ta birnin Paris Jean-Claude Gallet, ya fadawa manema labarai a gaban ginin a jiya Litini cewa, an kare muhimman ginshikan da ke rike da ginin.

Ya ce daya daga cikin ‘yan kwana-kwanan ya ji mummunan rauni yayin da ake kokarin kashe wannan babbar gobara a babban birnin na kasar Faransa.

Wutar, wadda a wani lokaci sai da ta yi sama da tsawon mita 10, ta lalata akasarin rufin majami’ar inda har hasumiyar rufin ta fadi.

Mai magana da yawun hukumar majami’ar, Andre Finot, ya gaya ma kafafen labaran Faransa jiya Litini cewa, ga dukkan alamu sai an karasa rusa duk wani abu dangin katako na cikin ginin majami’ar.

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG