Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Masana'antar Kannywood Take Kara’in Fitar Da Fina-finai


"Tsakaninmu" (Hoto: Ali Nuhu Instagram)

Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta tana ruwan fidda fina-finai a wani abu da masu lura da al’amuran da suka shafi harkar fim suke ganin bashi ne masana’antar take biya saboda cikas da annobar coronavirus ta haifar a bara.

Annobar coronavirus wacce ta bulla a karshen shekarar 2019 ta mamaye sassan duniya cikin shekarar 2020 take kuma ci gaba da yaduwa a kasashe da dama ta taka burki ga fannonin rayuwa da dama ciki har da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood da ke Najeriya.

Amma ga dukkan alamu, furodusohi, darektoci, jarumai da masu ruwa da tsaki a wannan masana’anta, sun dukufa wajen ganin annobar ba ta durkusar da wannan masana’anta ba wacce dubban matasa ke samun na kai wa bakin salati a karkashinta, take kuma nishadantar da miliyoyin mutane a sassa daban na duniya.

A lokacin da annobar COVID-19 ta yi kamari a bara, ba boyayyen abu ne cewa hankulan masu ruwa da tsaki da dama a masana’antar sun karkata wajen shirya fina-finai akan shafin Youtube (series,) abin da wasu ke alakantawa da irin tasirin da annobar ta yi akan masana’antar domin ba sai an je sinima ba.

Wasu na ganin hakan, abin alheri ne, domin ba ma tsoffin hannu kadai ba, matasa da dama sun samu kafar fito da dabarunsu na shirya fim, domin wasu da suke ganin ba su da kofar a dama da su a masana’antar, sun samu madogara ba tare da wani ya rike hannunsu ba.

Sai dai a gefe guda kuma, an ga karancin fitar da fina-finan da ake nunawa a sinima masu gajeran zango duk saboda dokar kulle da aka saka a wancan lokaci.

Izzar So (Hoto: Lawal Ahmad Instagram)
Izzar So (Hoto: Lawal Ahmad Instagram)

Masu bibiyar fim din Hausa, sun ga bullar fina-finan Youtube, irinsu Izzar So, Burin Raina, Zaman Aure, A Duniya, Kauran Mata, Talaka Bawan Allah, Babban Gida, Kaddarata da dai sauransu.

Masu sharhi kan harkar fina-finai na ganin zaman kulle da aka yi na tsawon watanni, su suka sa aka ga bullar ire-iren wadannan fina-finai a wani yunkuri na rufe gibin da aka samu sanadiyyar rashin fina-finai masu gajeran zango da aka saba gani, duk da cewa akwai daidaikun finan-finan ban dariya da akan samu a shafin na Youtube tun gabanin wannan annoba.

Ko da yake, wasu sun nuna cewa rashin riba da ba a samu ne a harkar, ya sa aka raja’a wajen shirya ire-iren wadannan fina-finai wadanda ake saka su a Youtube cikin sauki har ma a rika biyan wanda ya shirya fim din idan adadin masu kallon shafinsa ya kai wani shalli.

Duk da yake ana ci gaba da shirya iri wadannan fina-finai da ake saka wa a Youtube, tun a karshen shekarar 2020, manyan masu shirya fina-finai irinsu Ali Nuhu, Abubabakar Bashir (Maishadda,) Adam A. Zango, Sunusi Oscar 442, Sultan Abdulrraz dai sauransu suna ta rige-rigen fitar da sabbin fina-finai.

Tuni har an haska fim din “Bana Bakwai” na FKD Production, wanda ya ja hankalin jama’a da dama, fim din da ke dauke da manyan Jarumai irinsu Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Lawal Ahmad, Ramadan Booth da sauransu.

Hakazalika ana gab da sake sabon shirin “Farin Wata Sha Kallo” na Adam A Zango wanda tuni har an fara tallata shi.

Bana Bakwai (Hoto: Ali Nuhu Instagram)
Bana Bakwai (Hoto: Ali Nuhu Instagram)

Sannan an gab da haska fim din “Ranar Rabuwa” na kamfanin Abdul M. Sharif Movie, wanda Sunusi Oscar 442 ya ba dsa umurni.

Fim din na kunshe da jarumai irinsu, Abdul M. Shareeff, Halima Atete, Tijjani Faraga, Zainab Bauchi, Zainab Sambisa da sauransu.

Ranar Rabuwa (Hoto: Abdul M Shareef Instagram)
Ranar Rabuwa (Hoto: Abdul M Shareef Instagram)

Wani fim da shi ma aka kusan haskawa, shi ne “Tsakaninmu” na kamfanin Mai Shadda Resources, wanda Ali Nuhu y aba da umurni.

Farin Wata Sha Kallo (Hoto: Adam A Zango Instagram)
Farin Wata Sha Kallo (Hoto: Adam A Zango Instagram)

Sakin wadannan fina-finai da ma wadanda ke biye da su, alama ce a cewar masu sharhi da ken una masana’antar ta Kannywood tana kara’in fina-finan da ba ta sake a bara ba.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG