Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Najeriya Ke Kashe Dubban Biliyoyi Wajen Shigar Da Man Fetur


Hedkwatar kamfanin matatar man fetur Najeriya ta NNPC da ke Abuja a Najeriya
Hedkwatar kamfanin matatar man fetur Najeriya ta NNPC da ke Abuja a Najeriya

Adadin kudin da kasar ta kashe cikin watanni tara (wajen shigo da mai) ya kai kashi 28.3 cikin dari na kasafin kudin kasar da aka yi na naira triliyon 9.12 a shekarar 2018, a cewar rahoton.

Najeriya tana kashe naira tiriliyan 2.6 akan shigo da man fetur a cikin watanni tara.

Wani rahoto da hukumar kididdiga ta NBS ta fitar ya nuna cewa a tsakanin Janairu da Satumbar wannan shekara adadin kudin ya karu da kashi 12.9, wato Naira triliyon 2.289 da aka gani a zangon watannin uku-uku na farkon na shekarar da ta gabata.

Adadin kudin da kasar ta kashe cikin watanni tara (wajen shigo da mai) ya kai kashi 28.3 cikin dari na kasafin kudin kasar da aka yi na naira triliyon 9.12 a shekarar 2018, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Sannan ya kai kashi 36 cikin 100 na adadin kudin Naira triliyon 7.17 da aka bukata na karin kudin kasafi.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da hukumar matatar man kasar ta NNPC, ke cewa gwamnatin ta biya Dillan mai Naira biliyan 236, a matsayin wani kaso na farko daga cikin basussukan tallafin mai da dillalan ke bin gwamnatin ta Najeriya.

Mambobin kungiyar masu kula da depo-depo na mai da na dillalan man, DAPPMAN sun tabbatar da cewa gwamnati ta biya su wadannan kudade, kamar yadda suka tabbatarwa da jaridar Vanguard.

Wani jami’in kamfanin matatar man fetur din ta Najeriya, Mr. Henry Ikem-Obih, ya fadawa jaridar ta Vanguard cewa tun a ranar Larabar da ta gabata aka tanadi kudaden, wadanda suka fito a matsayin takardu masu daraja, kuma a ranar Litinin dillalan suka karba.

Amma ya ce, sai a watan Janairun badi za su zama tsurar kudi.

Saurari hirar da Ibrahim Ka'almasi Garba ya yi da mai fashin baki kan harkokin yau da kullum, Aminu Sule kan wannan batu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG