Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Rikici Ya Barke a Kamaru


Wani matashi kenan da ke jifar wasu yayin wata rigima da ta barke a kasar Isra'ila.
Wani matashi kenan da ke jifar wasu yayin wata rigima da ta barke a kasar Isra'ila.

A kasar Kamaru, an shiga zaman dar-dar a garuruwa da kuma kauyuka masu amfani da harshen Faransanci, wadanda ke makwabtaka da sashen masu amfani da Ingilishi.

Hakan na faruwa ne bayan da ‘yan tawaye masu gwagwarmayar kirkiro kasa mai amfani da harshen Ingilishi suka ketara zuwa yankin masu amfani da Faransanci suka kuma kashe sojojin gwamnati baya ga dumbin makaman da suka yi gaba da su.

Fararen hula a kasar sun bayyana cewa ba su ma da tabbas cewa sojojin gwamnati na iya kare su.

Alima Matembompo, wata manomiya ‘yar shekara 33, ta dinga zubda hawaye yayin da ake jana’izar mijinta a sashen masu amfani da harshen Faransanci a kauyen Galim da ke iyaka da yankin masu amfani da harshen Ingilishi.

Daga cikin mutanen da suka fito jana’izar mamacin, akwai wani mutum dan shekara 47 mai sayar da harawa, mai suna John Tatah, wanda ya ce tun bayan da aka kai harin aka rufe kasuwar kauyen.

"Akasarinmu masu sana’o’inmu duk sun durkushe, saboda haka muna addu’ar samun mafitar wannan tashin hankalin.”

Kasar Kamaru dai ta jima tana fama da tashe-tashen hankula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG