Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen ‘Yan Boko Haram A Sambisa


Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara

Shugaba Mohamadu Buhari yayi wa takwarorinsa na nahiyar Afirka albishir din cewa a watan Disambar nan ana sa ran sojojin Najeriya dana makwabtan kasar zasu afkawa dajin Sambisa domin gamawa da matsalar ‘yan Boko Haram lokaci daya.

Buhari yayi wannan jawabi ne a lokacin da yake ganawa da takwarorinsa na kasashen Afirka a Dakar ta kasar Senegal, a wajen wani taro da kungiyar hadin kan Afirka da wasu kungiyoyi na kasa da kasa suke shiryawa kowacce shekara domin yin nazari akan matsalolin zamantakewa da tsaro da kuma ci gaban nahiyar Afirka.

Kakakin shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu, yace shugaba Buhari yaje taron da sako ga shugabannin Afirka, na cewa su hade kansu don samun yakar sabbin matsalolin dake kunno kai a nahiyar, wanda suka hada da ta’addanci irin na kan teku.

Yanzu haka dai Najeriya ta sayo sabbin makamai da zasu taimaka wajen ganin an kawo karshen mayakan Boko Haram da suka rage.

Domin Karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00

XS
SM
MD
LG