Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Sojojin Najeriya Suka Kashe Kasurgumin Dan Fashin Daji Kachalla Gudau


Sojoji Najeriya yayin wani aikin sintiri a watan Mayun 2015.
Sojoji Najeriya yayin wani aikin sintiri a watan Mayun 2015.

Gudau ya taka muhimmiyar rawa wajen garkuwa da dalibai da ‘yan kasashen waje a kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe daya daga cikin kasurguman ‘yan fashin daji da suka addabi yankunan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Kwamshinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar ta Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da wannan galaba da sojojin kasar suka samu wacce ta yi sanadin mutuwar Kachalla Gudau.

“Kasurgumin dan bindigar nan Kachalla Gudau, wanda ke jagorantar gungun ‘yan fashin daji wajen yin garkuwa da mutane da kisa a kananan hukumomin Chikun, Kachia, da Kajuru, na daya daga cikin ‘yan fashin dajin da dakarun Najeriya suka kashe a ranar Lahadi a Kankomi da ke jihar Kaduna.” Aruwan ya ce

Gudau a cewar sanarwar, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da suka kai wani hari a yankin Kankomi, harin da sojojin Najeriya suka dakile suka fatattaki ‘yan bindigar har ya kai ga mutuwarsa a cewar Aruwan.

“An tsinci gawarsa (Gudau) a dajin Kankomi, wanda bisa ga dukkan alamu, ya mutu ne saboda yawan jinin da ya zubar.

“Sahihan bayanai sun yi nuni da cewa, bayan da ‘yan uwansa ‘yan fashin daji suka dauko gawarsa, sun yi jana’izarsa a yankin Dajin Kaku da ke Kaso a karamar hukumar Chikun.” Sanarwar ta Aruwan ta kara da cewa.

Kazalika wannan harin da dakarun Najeriya ta dakile, ya yi sanadin mutuwar wani “aminin” Gudau da ake kira “Rigimamme”.

Gudau ya taka muhimmiyar rawa a garkuwa da dalibai da ‘yan kasashen waje a kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia a jihar ta Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

XS
SM
MD
LG