Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wata Cuta Ta Kara Bulla a China


Wasu aladu
Wasu aladu

Masu bincike a kasar China sun gano wata cuta mai suna "Swine flu" (murar alade) da ka iya hadasa annoba a cewar wani bincike da aka wallafa a nan Amurka.

Cutar da aka yiwa lakabi da 4G, tana da alaka da sinadarin H1N1 da ya haddasa annoba a shekar 2009.

Cutar na da dukkan alomomin da kan iya harbin bil adama a cewar mawallafa, da malaman kimiya a jami’oin kasar China da cibiyar kare cututtuka masu yaduwa ta kasar.

Daga shekarar 2011 zuwa 2018, masu bincike sun dau samfurin majinar aladu dubu 30,000 wadanda aka yanka a mayanka da asibitin dabbobi a larduna 10 na kasar domin ba su damar kebe kwayoyin cutar 179.

Da yawa daga ciki an gano sabbabi ne kuma sun fi yawa a jikin aladu tun shekarar 2016.

A binciken da suka gudanar akan wani nau'in dabba ƙarama da ke farautar zomaye da ɓeraye, dabbar da ake yawan amfani da ita wajen gudanar da binciken da ya shafi mura, sabili da suma suna nuna alamun mura irin na kwayoyin cutar dake hadasa mura a jikin dan adam, kamar alamun zazzabi, da tari da atishawa.

An kuma gano G4 na da saurin yaduwa, kwayar cutar na da surin haihuwa ga saurin haifar da cuta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG