Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aiki: Kungiyoyin Kwadago, Gwamnati Na Tattaunawa


Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci
Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

A gobe Talata kungiyoyin ke shirin shiga yajin aikin na sai yadda hali ya yi, a wani mataki na nuna rashin jin dadinsu kan kin amincewa da gwamnati ta yi na biyan N30,000.00 a matsayin albashi mafi karanci.

Rahotanni daga Najeriya na cewa gwamnatin tarayya tana wata ganawa cikin sirri da wakilan kungiyoyin kwadago, a wani yunkuri na kaucewa shiga yajin aiki a gobe Talata.

Kungiyoyin na kwadago sun sha alwashin shiga yajin aikin idan har ba a fara biyan ma’aikata N30, 000.00 a matsayin albashi mafi karanci.

A baya, wakilan hadakar kungiyoyin kwadago da na ‘yan kasuwa a Najeriya sun kauracewa wani taro da gwamnatin tarayya ta kira domin kaucewa yajin aikin da kungiyoyin ke shirin yi, kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.

A farkon makon da ya gabata, kungiyar Gwamnoni ta yi tayin biyan N24,500.00 amma kungiyoyin na kwadago suka ki amincewa.

Masu lura da al’amura da fashin baki a fannin tattalin arziki, sun nuna fargabar cewa yajin aikin zai iya yin mummunan tasiri akan tattalin arzikin kasar.

Ma’aikata a Najeriya na karbar N18,000.00 a matsayin albashi mafi karanci, albashin da rahotanni ke cewa wasu jihohin ma ba sa iya biya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG