Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

“Yaki Da Boko Haram Ba Aikin Gwamnati Ba Ne Kadai”


Wasu sojojin Najeriya
Wasu sojojin Najeriya

Yayin da ake ta kiraye-kirayen a taimaka ma jami'an tsaron Najeriya a yaki da Boko Haram, rundunar sojin Najeriya ta ce dakura 'yan Boko Haram da aka yi ya sa su ke ta kokarin nuna cewa har yanzu su na da karfi, ta wajen kai hare-hare.

Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Manjo-Janar Tukur Yusuf Brutai ya ce wutar da ‘yan Boko Haram ke sha ce ta sa su shiga kai hare-haren kunar bakin wake don su nuna har yanzu sun a nan, alhalin kuwa tasu ta kusa karewa.

Don haka wakiliyarmu a shiyyar Filato Zainab Babaji ta tuntubi wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum mai suna Dan Manjang don jin yadda yak e ganin al’amuran tsaro a Najeriya a yanzu sai ya yi nuni da kudurin Janar Burutai na cimma wa’adin da Shugaba kasa a ba sojojin Najeriya. To amma y ace kodayake akwai fatan a gama da Boko Haram cikin wa’adin na Shugaban kasa, da wuya a iya cimma wannan wa’adin. Y ace ai ba a Naijeriya kawai Boko Haram su ke ba.

Game da cigaba da kai hare-haren da ‘yan Boko Haram ke yi, Manjang y ace ya kamata mutane su gane cewa yaki da ta’addanci ba aikin gwamnati ba ne kawai, na kowa da kowa ne. Y ace ba jami’an gwamnati ‘yan ta’addar ke kashewa ba, jama’a ne; kuma gashi babu yadda ‘yan ta’addar za su shiga cikin jama’a ba tare da sanin kowa ba. Ya ce da gwamnati da jama’a - kowa da rawar da ya kamata taka.

Ga Zainab da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG