Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Talauci: Wata Majami’a Ta Bude Bankin Al’umma


Damin Naira
Damin Naira

A cigaba da bayar da gudunmowa da kungiyoyin addinai su ke yi ga bangarorin tattalin arziki da zamantakewa a Najeriya, wata Majami'a a jahar Adamawa ta yinkuro ta kafa wani bankin al'umma. To amma Majami'ar ta ce banki zai yi hulda da mai bin kowani irin addini saboda hada kan jama'a da kuma karfafa marasa karfi.

A wani yunkuri na taimakawa wajen yaki da talauci da kuma samar da ayyukan yi ga matasa, babbar Majami’ar EYN a Najeriya ta kaddamar da wani sabon bankin taimakawa al’umma, mai suna Brethren Micro Finace Bank, a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Tun bayan kafa bankin Ja’iz sauran kungiyoyin addinai a Najeriya sun bi sahu wajen kafa wasu kananan bankuna domin tallafawa masu karamin karfi da ke son soma sana’a dama samar da ayyukan yi ga matasa wanda hakan, a ganin masu lura da al’amura, zai taimaka wajen kawo kwanciyar hankali da cigaba ta fannin tattalin arziki da zamantakewa.


Bisa ga bayanin Majami’ar ikliziyar yan uwa ta EYN, bankin na Bretheren Micro Finance Bank, wanda cibiyarsa zata kasance a jihar Adamawa, zai yi ta yado ne sannu a hankali. A wajen taron kaddamar da shugabanin hukumar gudanarwar bankin a Yola, Shugaban Majami’ar a hajar ta Adamawa, Rabaran .Joel Bili, ya ce an kirkiro bankin ne domin samar da aikin yi da bunkasa kananan sana’o’in dogaro da kai musamman tsakanin matasa, mata da marasa karfi ta tare da la’akari da addinin mutum ba. Mrs Viginia Lazarus Zoaka wadda ita ce shugabar kwamitin gudanarwar bankin, ta ce bankin zai kyautata wa wadanda ke hulda da shi.

To ko shin ma wannan banki da cocin ya kafa ya cika dukkanin sharuddodi da ka’idojin da babban bankin Najeriya, CBN, ya gindaya kuwa? Chief Marsha Zoaka, jagoran kwamitin kwararrun bankin, ya ce an cika sharuddan. Ya ce babban bankin na Najeriya ya yi ta bibiyar abubuwan da ke faruwa da zummar daukar mataki ko yin gyara. Ya ce kafin ma a nada kwamitin amintattun bankin sai da aka binciki kowannensu saboda kar a yi kitso da kwarkwata.

Ga dai Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG