Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Ya Kare A Kasar Iraqi


Shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana cewa daga wannan rana, Amurka ta kawo karshen dukkan matakan soja a kasar Iraqi, kamar dai yadda yayi alkawarin zai yi a lokacin yakin neman zabe

Shugaba Barack Obama na Amurka ya ce an kawo karshen matakin farmakin sojan da Amurka ta kai kan kasar Iraqi a shekarar 2003, kuma daga yau yakin kasar Iraqi ya kare ke nan.

A cikin jawabin da yayi ga kasa ta telebijin dazu daga ofishinsa a cikin fadar White House, shugaba Obama yace wannan abin tarihi na kawo karshen yakin Iraqi, ya zo a daidai lokacin da Amurkawa da dama suke bayyana rashin sanin tabbas game da makomarsu, a bayan da aka yi kusan shekaru 10 ana yaki tare da fuskantar koma-bayan tattalin arziki.

Ya ce abubuwa da yawa sun canja tun lokacin da tsohon shugaba George W. Bush ya kaddamar da yaki kan Iraqi a watan Maris na 2003, yana mai fadin cewa yakin da aka fara da nufin kwance damarar yakin wata kasa, sai ya koma yaki da 'yan tawaye da tsagera.

A cikin wannan jawabin nasa, shugaba Obama ya ayyana karshen yaki a kasar Iraqi, ya kuma ce daga yau, nauyin tsaron kasar ya koma hannun 'yan Iraqi.

A yayin da yake ayyana wannan kuma, shugaban ya lura cewa yakin Iraqi ya zamo daya daga cikin yake-yake mafi daukar lokaci da Amurka ta taba yi. Amma yace a duk tsawon shekarun, sojojin Amurka, mazansu da matansu, sun sadaukar da kai suka yi aiki tukuru ma kasarsu.

Shugaban ya ce a matsayinsa na babban kwamnadan sojojin Amurka, yana mai alfahari sosai da irin wannan sadaukar da kai na sojojin Amurka, kuma kamar sauran Amurkawa, shi ma kansa ya rasa abinda zai ce da irin wannan sadaukar da rai nasu da na iyalansu.

Sojojin Amurka su na horas da sojojin Iraqi a Bagadaza
Sojojin Amurka su na horas da sojojin Iraqi a Bagadaza

Yace Amurkawan da suka yi aiki a Iraqi, sun gudanar da dukkan ayyukan da aka umurce su da su gudanar, suka kuma kawar da gwamnatin da ta yi ta muzgunawa al'ummarta. Shugaba Obama yace sojojin Amurka da na kasashen kawance da kuma na Iraqi, sun yaki abokan gaba titi-titi, gida-gida domin taimakawa 'yan Iraqi wajen inganta makomarsu.

Ya ce a yanzu, Iraqi tana da damar rungumar sabuwar makoma, koda yake akwai kalubale da yawa a gabanta.

Mr. Obama yace da ma tun yana yakin neman zabe, yayi alkawarin kawo karshen wannan yaki na Iraqi. Ya ce gwamnatinsa ta janye sojojin Amurka kusan dubu 100 daga Iraqi, ta rufe daruruwan sansanonin soja a Iraqi ko ta mika su ga sojojin Iraqi, ta kuma kawar da miliyoyin kayayyakin soja daga kasar.

Yace koda yake har yanzu Iraqi tana ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci, irin wadannan hare-haren sun ragu sosai fiye da kowane lokaci tun fara yakin.

Yayi kira ga shugabannin Iraqi da su gaggauta daukar matakin kafa gwamnati wadda zata kunshi kowa da kowa a kasar. Ana fuskantar daurin gwarmai na siyasa a Iraqi tun watan Maris a bayan da aka kasa samun wani fitaccen dan takara da yayi nasara a babban zabe.

XS
SM
MD
LG