Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawan Nijar Sun Ga Kasawar Gwamnatin Issoufou Mahammadou


Shugabannin kawancen 'yan adawan Nijar
Shugabannin kawancen 'yan adawan Nijar

A taron gangamin da 'yan adawan suka yi a karshen mako a Nijar, jam'iyyun adawan a karkashin kawancen FRDDR sun nuna rashin gamsuwa da yadda alamuran mulki ke gudana a kasar Nijar.

'Yan adawan sun dora laifin kasawar gwamnatin kasar ne akan shugaban kasa Issoufou Mahammadou wanda suka ce cika alkawuran da yayiwa talakawa lokacin neman zabe ya faskareshi.

Alhaji Dudu Muhammadou na sabuwar jam'iyyar FDR Canji ya bada misalan gazawar gwamnatin Issoufou Mahammadou. Na farko shi ne batun samar da kwamciyar hankali a cikin kasar. Yace suna zaune lafiya da amma sai aka wayi gari shugaban kasar ya kawo masu rashin zama lafiya.

Kafin Issoufou ya hau mulki yayi alkawarin ba kowane yaro ilimi kyauta na shekaru goma sha shida. Yayi alkawarin bada magunguna kyauta wanda bai cika ba. Haka ma lamuran kasuwa ya tabarbare a arkashin gwamnatin Issoufou.

Gangamin 'yan adawan Nijar
Gangamin 'yan adawan Nijar

Jam'iyyun na adawa sun bukaci Shugaba Issoufou Mahammadou da ya sauka daga kujerar shgabancin kasar ta Nijar saboda a cewarsu ya gaza.

Saidai jam'iyyar PNDS mai mulki tayi watsi da bukatar ta 'yan adawa. Alhaji Umaru na PNDS din yace batun na 'yan adawan irin na wadanda dabara ta kubuce masu ne.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG