Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Kan Iyakar Najeriya


Wani yankin jihar Bornon Najeriya da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari a baya

Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun halaka mutane 15 suka kuma yi garkuwa da wasu mutane takwasa a wani kauye da ke kusa da iyakar Najeriya a yankin garin Kolofota na kasar Kamaru.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun harbe mutane 15 har lahira, kana suka yi garkuwa da wasu takwas a wani kauye da ke arewacin kasar Kamaru.

Jami’ai sun ce ‘yan bidigar sun yi ta bude wuta ne akan kauyen Gakara da bindgogi masu sarrafa kansu, da tsakar daren Alhamis har zuwa wayewar garin Juma’a, sannan suka kona gidaje sama 30.

Shi dai kauyen na Gakara, yana wajen garin Kolofata ne, wanda ya sha fama da hare-haren ‘yan kungiyar ta Boko Haram, yana kuma da iyaka da Najeriya.

Jami’an cikin gida a kasar ta Kamaru, sun ce mutane da dama sun tsere daga kauyen inda suka nemi mafaka a sansanin ‘yan gudun hijirar da ke Kolofatan, wanda ke dauke da dubban mutane da suka tserewa rikicin Boko Haram.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kungiyar ta Boko Haram ta sha kai hare-hare a Kamaru da Jamhuriyar Nijar da Chadi, lamarin da ya kai ga kasashen suka kafa wata rundunar tsaro mai hadakar dakaru 8,700 domin tunkarar kungiyar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG