Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Na Harbin Dauki Dai-Dai A Kudancin Jahar Taraba


Hoton bindigogi

A gonakin bayan garin karamar hukumar ta Ibbi maharan ke labewa su na harbin duk wanda suka hanga

Yanzu haka ana cikin tashin hankali da zaman dar-dar a kudancin jahar Taraba biyo bayan harbin-dauki-dai-dai da wasu 'yan bindiga ke yiwa jama'a a yankin karamar hukumar Ibbi.

Maharan sun kashe wasu manoma a bayan garin Ibbi cikin irin hare-haren da suke kaiwa, musamman ma a bayan garin Ibbi.

Shugaban karamar hukumar Honorable Isiaka Adamu ya tabbatar da faruwar wadannan hare-hare, kuma ya gargadi jama'a da su guji fita bayan gari, ko zuwa kauyukan da ke bayan garin na Ibbi domin kar maharan su rutsa da su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Yanzu haka dai an tura jami’an tsaro sun bi sawun maharan, 'yan bidiga da nufin gano inda suke, kuma su farauto su.

Wakilin Sashen Hausa a jahohin Adamawa da Taraba Ibrahim Abdulaziz ne ya hada wannan rahoto.

XS
SM
MD
LG