Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 27 A Jihar Filato


Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a kauyen Kidoro, dake yankin Irigwe dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato, inda suka hallaka akalla mutane ashirin da bakwai ciki harda mata da kananan yara.

Da asubahin yau litini ne lamarin ya faru kan mutanen da basa dauke da makamai kwanaki kadan bayan jihar Filato ta kafa dokar hana yawo daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a karamar hukumar Bassa, biyo bayan yawaitar kashe-kashen da ake yi a yankin.

Mai ba gwamnan jihar Filato shawar kan harkokin yada labarai Mr Dan Manjan, ya ce lamarin ya kasance abin takaici kwarai saboda dumbin rayukan da ke salwanta a wasu sassan jihar.

Shugaban matasa kabilar Irigwe, Ayuba Chinge, ya bayyanawa wakiliyar sashen Hausa na Muryar Amurka Zainab Babaji cewa mutanen da aka hallaka na zama a wata makarantar Firame ne karkashin kulawar wasu sojoji, kawo yanzu mutane ashirin da bakwai suka hallaka, wasu da dama kuma na kwance a asibiti.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Ummar Dakare, ya bayyana cewa babu hannun Fulani a cikin lamarin kuma ya yi kira ga daukacin Fulanin yankin da kada su dauki doka a hannunsu, su kasance masu biyayya ga gwamnati.

Daga jihar Filato, Zainab Babaji ta aiko mana da cikakken rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG