Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Sojojin Masar Wajen 30


Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi

An yi ma wasu 'yan sandan Masar kofar rago, inda aka hallaka 30 daga cikinsu yayin da su ke kokarin farautar 'yan zafaffiyar kungiyar nan ta Hasm, wadda ta yi ta gasa ma gwamnatin kasar aya a hannu tun bara.

:'Yan sandan kasar Masar akalla 30 sun hallaka, a wata musayar wuta da wasu 'yan bindiga a yankin hamadar kasar da ke yamma.

Jami'an tsaro su ka ce an bude ma 'yansandan wuta ne, yayin da su ke binciken zakulo 'yan kungiyar Hasm, wadda ta dauki alhakin kai hare-hare da dama a Masar din bara.

Jami'an sun ce wasu 'yansandan kuma 8 sun samu raunuka a wannan harin, wanda ya faru a gundumar al-Wahat al-Bahriya, mai tazarar kilomita 135 kudu da birnin Alkhahira.

Wata takardar bayani daga Ma'aikatar ciki gida ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ta ce an hallaka wasu 'yan bindigar ma.

A cewar kafar labarai ta AFP, kungiyar ta Hasm ta dauki nauyin kai wannan harin.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG