Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Zamfara


Wasu makiyaya.
Wasu makiyaya.

Ana kyautata zaton Fulani makiyaya ne suka kai farmaki lokacin sahur a karamar hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

'Yan sanda sun ce an kashe mutane akalla 7 a lokacin da wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne suka kai farmaki lokacin sahur a kan wani gari mai suna Gidan Dawa dake yankin karamar hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

Wasu majiyoyin sun fadawa wakilinmu cewa watakila wannan farmaki da aka kai da asubahin talata, ba zai rasa nasaba da wata mummunar gardamar da aka yi tsakanin mutanen wannan gari da kuma wasu Fulani makiyaya da suka wuce ta garin kwanakin baya ba.

Mutanen garin dai sun ce yawan wadanda aka kashe ya zarce mutum 40, amma kakakin 'yan sandan Jihar Zamfara, DSP Lawal Abdullahi, yace jami'ansu su na garin ma a lokacin da aka binne mutanen da suka mutu.

Yace 'yan sanda sun fara bincike, kuma yana da kwarin guiwar cewa nan bada jimawa ba zasu kamo wadanda suka aikata wannan ta'asa. Yayi kira ga jama'a da su guji daukar doka a hannayensu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG