Accessibility links

A Najeriya Wasu 'Yan Bindiga Sun Harbe Akalla Mutane 6 A Wani Coci cikin Jihar Yobe.

  • Aliyu Imam

Ginin wani coci da aka kaiwa hari a Kaduna
A Najeriya, ‘yan bindiga a arewa maso gabashin kasar, sun kashe akalla mutane shida cikin daren talata, sa’adda suka bude wuta kan wani coci, lokacinda ake ibadar shigar kirsimeti.

Jami’ai da mazauna wurin suka ce an kai harin ne bayan tsakar dare a wani kauye dake wajen birnin Potiskum cikin jihar Yobe. Babu wani ko kunigya data fito nan da nan ta dauki alhakin kai wannan hari.

Jihar Yobe makwabciyar jihar Bornio ce, inda nan ne helkwatar kungiyar Boko Haram mai zazzafar ra’ayi. Kungiyoyin kare hakkin BilAdama suka ce kungiyar ta kashe fiyeda mutane dubu daya cikin shekaru hudu d a suka wuce.

Kungiyar Bokon Haram tana auna hare harenta ne kan coci coci lokacin kirsimeti a a 2010 da kuma bara. A harin da kungiyar ta kai bara ta kashe fiye da mutane 40.

Kungiyar tana yaki da nufin kafa tsarin shari’a a arewacin Najeriya, inda galibi mazauna yankin musulmi ne.

A cikin hudubar kirsimeti d a ya gabatar a jiya talata, Papa Roma Benedict yayi addu’ar zaman lafiya a Najeriya inda yace ayyukan ta’addanci na salon kauyenci yake rutsawa da mutane, musamman a tsakankanin kiristoci.
XS
SM
MD
LG