Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Libya


 Bernardino Leon, Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan Libya
Bernardino Leon, Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan Libya

Yayin da Majalisar Dinikn Duniya ke kokarin gudanar da taron tattanawa tsakanin 'yan gwagwarmaya da gwamnati sai gashi an sace mataimakin ministan harkokin wajen kasar

An soma wani sabon shirin tattaunawa tsakanin ‘yan gwagwarmaya da gwamnatin kasar Libya duk da cewa wasu sun yi garkuwa da mataimakin ministan harkokin wajen kasar.

A wani yunkurin lalubo zaren warware rikicin Libyan, Majalisar Dinkin Duniya tace za’a yi zaman tattaunawar sau biyu. Zaman farko za’a yishi a kasar Switzerland.

Dama can tawagar gwanmnatin Libya da Firayim Ministan kasar Abdullah al-Thani ya jagoranta ta zanta da ‘yan gwagwarmayar makonni biyu da suka gabata. To saidai kungiyar hamayyama fi girma bata kasance a taron ba.

Kungiyar ce ta cafke Birnin Tripoli bara lamarin da ya tilastawa Firayim Ministan al-Thani ficewa daga Birnin ya je ya kafa gwamnatinsa a gabashin kasar.

Ana cikin wannan sabon kokarin sasantawa sai kuma jiya Lahadi ‘yan bindiga suka cafke mataimakin ministan harkokin wajen kasar Hassan al-Saghir daga dakinsa a wani otel dake Birnin al-Baida. Jami’an gwamnati sun shaidawa manema labarai cewa ‘yanbindigan sun gayawa ma’aikatan otel din cewa su dakarun gwamnati ne.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin yin garkuwa da ministan.

XS
SM
MD
LG