Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Kananan Yara Bakwai a Adamawa


Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun kai hari a wani kauye inda suka kashe mutune tara da kuma yin awon gaba da wasu kananan yara bakwai.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar wasu yan bindiga da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne a jihar Adamawa, yanzu haka sun soma addabar al’ummomin yankin kananan hukumomin Fufore da Jada, inda suka yi dirar mikiya a kauyen Iware dake kusa da Beti-Verre dake tsakanin Fufore da Jadana, suka kashe mutune tara da kuma sace kananan yara bakwai.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa a cikin dare aka kai farmakin.

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta bakin kakakinta SP. Othman Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da sa ido.

A baya dai irin wadannan ya bindiga sun taba garkuwa da wani dan Majalisar dokokin jihar, dake zama kanin tsohon shugaban hukumar EFCC, Mallam Nuhu Ribadu, don neman kudin fansa.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG