Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindigar Zamfara Sun Sake Tabka Kazamar Ta’asa; Sun Kashe Mutane 13


Wasu 'yan bindigar da aka kama kwanan baya a Zamfara.

Yayin da ake cewa 'yan bindigar Zamfara sun gudu zuwa wasu jahohi saboda jami'an tsaro sun takura su, sai kuma gashi ana ta samun rahotannin da ke nuna alamar ba su gudu ba. Hasali ma, sai cigaba da gallaza ma jama'a su ke yi.

A wani al’amari mai daure kai, wasu mahara, wadanda wasu ke zargin cewa ‘yan yankin ne, sun sake kai hari a kauyen Gidan Kaso da ke Karamar Hukuma Birnin Magaji ta jahar Zamfara, inda su ka kashe mutane akalla 13 baya ga wadanda su ka ji ma raunuka da kuma dukiyar da au su ka sace au su ka barnata.

Wasu ganau kuma mazauna kauyen na Gidan Kaso, wadanda su ka bukaci a sakaya sunayensu saboda tsoron abin da ka biyo baya, sun ce maharan sun isa garin ne da babura kuma sabe da bindigogi da yammacin jiya Asabar su ka shiga bude wuta da kuma kone-kone. Su ka ce kusan duk wayewar gari sai wadannan maharan sun far ma wasu mutane a yankin. Su ka ce saboda yawan kai hare-haren da mutanen ke yi, har manoman yankin sun kasa zuwa gonakinsu duk kuwa da damina ta kankama.

‘Yan yankin su ka ce idan ma an girke sojoji a Birnin Magaji, kamar yadda hukumomi ke ikirari, to girke sun bai yi wani tasiri ba – a kalla ya zuwa yanzu dai. Haka ma jiragen sintirin da ke tauna tsakuwa a yankin; sun ce bas u hana miyagun cin karansu ba babbaka.

Duk wani kokari na jin ta bakin ‘yan sanda ya ci tura.

Ga wakilin Muryar Amurka, Mustala Sanyinna, da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG