Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Boko Haram sun kai hari garin Miringa


Wasu maza da ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne

Wasu da ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai hari garin Miringa, a jihar Bornoi suka kashe mutane takwas a ranar Laraba da dare

A daren ranar Laraba, wasu mahara wadanda ake kyautata zaton yan kungiyar Boko Haram ne, sun apkawa garin Miringa dake karamar hukumar Biu a kudancin jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria, suka kashe mutane 8.

An kai wannan harin ne, bayan harin da aka kai garin Buratai, mahaifar hafsan sojojin Nigeria Janaral Tukur Buratai, A wancan harin an kashe mutane biyu.

Washegarin wannan harin, wata mace da ake zaton 'yar kunar bakin wake ce ta tarwatsa kanta a kofar shiga birnin Biu, inda ake binciken ababen hawa.

Wani mazaunin garin Miringa ya shedawa wakilin sashen Hausa cewa tun goshin mangariba aka fara ganin maharan sun fara shigowa garin. Sa'anan zuwa bayan sallar mangariba, wadanda suka shiga garin sun kai mutane 20.

Yace daya daga cikin maharan ya shiga garin akan babur. Sauran kuma sun shiga garin cikin motoci. Suka kashe mutane 8 a unguwar Pompamari. Yace a lokacin da suka harin babu sojoji a garin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

XS
SM
MD
LG