Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Manoma Biyu, Sun Sace Biyu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun shiga wani kauye mai suna Alau mai tazarar kilomita biyar daga Maiduguri, babban birnin jahar Borno, su ka yi ma wasu manoma biyu yankar rago su ka kuma sace wasu biyu.

Tashin hankalin da ya biyo bayan wannan al’amari ya sa wasu magabatan wannan gari, bisa jagorancin wakilin Lawanin garin, sun ruga birnin Maiduguri inda su ka tuntubi hukumomi da ‘yan jarida. Wakilin Lawanin garin mai suna Babakura Lawan, ya gaya ma manema labarai cewa ba a san inda aka kai wadanda aka sace din ba. Ya ce wadanda aka kashe din su ne Bulama Musa da Madu Abba Musa Gulumba kuma manoma ne da aka sansu sosai a garin.

Wakilin Bulaman ya ce tun ba yau ba ake ta gaya ma hukumomi yanayin tsaro a yankin ba tare da an dau wani mataki ba. Ya ce wani sa’in ma har kama mutane ake yi a je a zuba su cikin kwale-kwale a watsar da su cikin ruwa. Shi ma Kansilan wurin, wanda aka sakaya sunansa, ya ce rabin kayan abinci da ake kaiwa birnin Maiduguri daga kauyen na Alau su ke fitowa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG