Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kashe Masuntan Kamaru Guda Uku


Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya

Maharan Boko Haram sun sake kai wani farkami a Dara, wani gari da ke kan iyaka da Najeriya da Cameron.

Inda har suka kashe wasu mutane guda uku masu sana'ar kamun kifi. Sannan mazauna wadannan yankuna na kan iyakar Cameroon da tafkin Chadi suna ta kokawa yadda tsaro ya faskara a wannan waje.

Ko a jiya bisa rahotanni sai da 'yan Boko Haram din suka kashe wasu mutane guda biyu a wannan yanki suka kuma tsere zuwa cikin Najeriya.

Alhaji Ya'u wani masani ne a game da harkokin tsaro a birnin Marwa, inda ya yiwa Wakilinmu Muhammad Auwal Garba karin haske akan yadda ya kamata a shawo kan wannan lamarin.

Ga cikakken rahoton a makalar sauti ta kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00
XS
SM
MD
LG