Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kashe Matasa 'Yan Banga 14 A Bama


Watamotar soja tana gadi a kifar wani gida da aka kona a garin Bama, Jihar Borno, ran 7 Mayu 2013

Wani jami'i yace 'yan Boko Haram sun yi shigar soja, suka yaudari matasan 'yan banga zuwa wani wurin da suka kashe su, suka raunata guda 9.

Wani jami'in yanki ya fada litinin cewa 'yan bindiga na kungiyar Boko Haram sun kashe matasa 14 masu aikin banga da farautar 'yan Boko Haram a garin Bama, dake Jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan lamarin ya faru ne ranar lahadi, abinda ke haddasa tababa a kan ko za a iya samun nasarar cimma gurin murkushe ayyukan kungiyar afarmakin da sojoji ke kaiwa.

Kungiyoyin matasa 'yan banga da ake kira "Civilian JTF" wadanda matasa
'yan sa kai suka kakkafa, sun taimaka ma sojoji fiye da komai wajen kamo 'yan Boko Haram. Sai dai kuma wannan ya sa a yanzu 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram sun fara auna makamansu a kan wadannan matasa.

Shugaban majalisar karamar hukumar Bama, Alhaji Baba Shehu Gulumba, ya fadawa 'yan jarida a Maiduguri, babban birnin Jihar cewa 'yan bindigar sun yi shiga irinta sojoji, suka yaudari matasan dake gadi a lokacin zuwa wani wuri dabam da sunan yin taro, suka bude wuta suka kashe 14 cikinsu. Wasu guda 9 sun ji rauni.

Yace, "(matasan) su na aikin gadi a lokacin da 'yan Boko Haram suka zo cikin kayan soja, suka ce musu ana bukatarsu a wurin wani taron da za a yi a nan kusa. A lokacin da aka yaudare su suka bar inda suke aikin na gadi, sai aka kai musu farmaki aka kashe su."

Garin Bama, ba ya da nisa daga wasu duwatsun dake bakin iyakar Najeriya da Kamaru, inda aka yi imanin 'yan Boko Haram da dama sun buya, a bayan da sojoji suka baza su cikin daji daga sansanoninsu na da.

A makon jiya, rundunar sojojin Najeriya ta ce watakila dai shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu a tsakanin Yuli zuwa farkon watan Agsuta a dalilin rayunukan harsasai da ya samu yayin wata gwabzawa makonni da dama kafin nan.

Idan har da gaske ne ya mutu, da alamun mutuwar tasa ba ta dakile tashin hankalin ba, maimakon haka ma, munanan hare-hare sun karu ne fiye da wata gudan da ya shige.

A ranar litinin na makon jiya, wasu da ake jin 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane akalla 44 dake salla cikin wani masallaci a kauyen Bemba a kusa da tbkin Chadi.
XS
SM
MD
LG