Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Yan Boko Haram Sun Sake Sace Mutane


'Yan Boko Haram
'Yan Boko Haram

Rahotanni daga arewacin jihar Adamawa, a arewa maso ganashin Najeriya, na cewa mayakan Boko Haram sun sake kai hari garin Michika, inda suka ta kone kone da kuma kashe jama’a.
Wannan kuma na zuwa ne yayin da dakarun sojojin Najeriuya, ke kokarin kwato sauran kananan hukumomi, biyu dake hannun yan Boko Haram, a jihar ta Adamawa.

Wasu da suka tsallake rijiya da baya sun yi bayanin cewa bayan wadanda aka kashe, anyi awon gaba da wasu mutane da dama, haka nan kuma ‘yan kungiyar ta Boko Haram, sun yi mummunar ta’adi, a garin inda suka kona gidaje da dama.

Sun kara da cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram, sun samu cin karansu babu babbaka ne saboda babu jami’an tsaro a yankin na Michika, alokacin da ‘yan kungiyar suka farwa garin.

Michika Boko Haram - 3'03"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

XS
SM
MD
LG