Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fashi A Jamhuriyar Benin Sun Afkawa Makabarta Fiye Da Dari Suna....


A Benin ‘yan fashi sun tone kaburbura fiye da dari a wata makabatara dake kusa Porto-Novo babban birnin kasar, a wasu lokutanma har suna yanke wasu sassan gawarwakin.
Hukumomin kasar sun fara binciken sace sacen ne a a wani kauye da ake kira Dongbo, bayan da wani birkila da yake aiki a makabartan ya tuntubi ‘Yan sanda.

A hira da Muriyar Amurka ranar jumma’a, wani wakilin a tashar talabijin a Benin Charlot Ogou, yace barayin sun yanke kawunan wasu gawarwakin.Yace wannan shine karo na farko cikin shekaru biyar da aka aikata irin wannan satar.

Wakilin yace ‘Yan sanda basun tantance dalilin satar ba, kuma sun ki suce ko sace sacen gawarwakin yana da nasaba da tsafe-tsafe da ya tsananta. Wannan lamari yana da karfi sosai a kasar.
XS
SM
MD
LG