Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fashin Teku Sun Kama 'Yan Najeriya Tara


Wasu 'yan feshin teku sun kai wa wani jirgin ruwan dakon mai da tace shi daura da gabar Najeriya, tare da kama wasu 'yan Najeriyar 9.

Ana wa Jirgin ruwan na Sendje Berge wasu gyare-gyare ne a lokacin da aka kai harin a cewar wani babban jami'i na kamfanin BW Offshore mai mallakar jirgin ruwan.

Kamfanin mai hedikwata a Oslo ya ce babu wani daga cikin sauran mutanen da ke cikin jirgin ruwan da ya samu rauni.

"Muna aiki yanzu da hukumomin Najeriya domin ceto 'yan Najeriyar nan da aka yi awon gaba da," a cewar Andreassen.

Jirgin, wanda ke tace danyen mai da kuma adana shi duk a bisa ruwan, wanda kuma ke iya samar da gangar mai 50,000 a kullun, na aiki ne a rijiyoyin mai na Okwori, da kamfanin man Addax, reshen babban kamfanin Sinopec na China, ke gudanarwa.

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG