Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira Daga Jihohin Dake Da Dokar Ta Baci Na Zuwa Jamhuriyar Nijar


Mata suna kokarin ketare hanya bayan an ayana dokar ta baci a Maiduguri.

Kawo yanzu mutane fiye da dubu biyu da dari hudu ne suka kwarara cikin Jamhuriyar Nijar daga jihohin Borno da Adamawa da Yobe saboda da dokar ta baci da gwamnatin Najeriya ta saka wa jihohin.

Kawo yanzu mutane fiye da dubu biyu da dari hudu ne suka kwarara cikin Jamhuriyar Nijar daga jihohin Borno da Adamawa da Yobe saboda da dokar ta baci da gwamnatin Najeriya ta saka wa jihohin.

Yunkurin Kakkabe 'yan bindiga da sojoji ke yi ya tsorata mutane, don haka ne suka arce daga gidajensu. Yawancin wadanda suka nemi mafaka a Nijar mata ne da yara.

Akwai rahoton dake cewa wasu na shiga Najeriya da safe kana da yamma su koma Nijar.

Rahotanni da Muryar Amurka ya samu sun ce an ga jerin gwanon motoci da kayan agaji akan hanyarsu zuwa wadanda ke gudun hijirar.

Hukumomin Nijar sun ce yawanci 'yan gudun hijiran, Filani da Barebari, suna zaune ne da yan’uwa wato babu wani sansani na musamman na 'yan gudun hijirar.

Abdullahi Maman Ahmadu na da karin bayani a wannan rahoton.

Yan gudun hijira daga Najeriya suna kwaraa zuwa cikin Jamhuriyar Nijar - 2:43
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG