Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan gudun hijira sun bi ta kan 'yan sanda a Macedonia


Yan gudu hijira suna kokarin wuce yan Sanda akan iyakar Macedonia

A ranar Asabar dubban 'yan gudun hijira suka bi ta kan yan sandan kasar Macedonia wadanda suke dauke da kulake. Yan sandan sun yi kokarin hana yan gudun hijira shiga kasar daga kasar Girka

Jiya Asabar dubban yan gudun hijira suka bi ta kan yan sandan Macedonia dake dauke da kulake, wadanda suka yi kokarin hana su shiga kasar daga kasar Girka. Yan sanda sun harba gurnatin giri kuma mutane da dama sunyi rauni a arangamar da aka yi akan iyaka.


Jami'an tsaro sun samu nasarar tare daruruwan yan gudu hijirar, amma dubban su yawancinsu yan kasar Syria sun ratsa suka shiga yankin Macedonia bayan suyi kwanaki suna zaune a filin Allah ta'ala, ba tare da samu ruwa ko abinci ko kuma wurin kwana ba

.
An fara hargitsin ne a lokacinda 'yan sanda suka yanke shawarar barin wasu yn gudun hijira masu kanana yara su wuce, Sai wadanda suke baya suka kutsa kai

.
Sai kuma dubbai ciki harda mata rike da jarirai da kuma maza dake dauke da kanana yara, suka yi amfani da damar da suka samu, suka yi ta gudu a filin da babu waya suka shiga yankin kasar Macedonia.


Daga baya yan sanda sun samu damar shawo kan al'amarin suka hana kwarara yan gudun hijira bayan da suka mintoci talatin suna harba gurnatin giri.
Wadanda suka samu nasarar kutsawa kasar sunyi caa suka doshi birnin Gevgelia inda suka shiga taxi taxi da wasu motocin safa suka doshi Serbia akan hanyarsu ta zuwa kan iyakar kasashen turai


A ranar Alhamis kasar Macedonia ta ayyana dokar ta baci kuma ta bada umarnin a rufe kan iyakokinta kada a bari yan gudun hijira su shige, yawancin yan gudun hijiran, suna arcewa yaki kuma suna shiga ne ta kasar Girka.

Kusan mutane dubu biyu ne ke tsalaka kan iyaka kulu yaumin akan hanyarsu ta zuwa kasar Hungary da yankin kasashen turai da ba iyaka.

XS
SM
MD
LG