Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gwagwarmaya A Syria Suna Zargin An Kashe Fiyeda Mutane 50


Hayaki yake tashi a Al Hader dake yankin Hama,

Kungiyoyin hakkin Bil Adama sun yi zargin cewa sojin Gwamnatin Syria sun kashe mutane akalla hamsin da biyar a wani harin kan mai uwa da wabin da suka kai kan garuruwa biyu inda masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Bashar al-Assad.

Kungiyoyin hakkin Bil Adama sun yi zargin cewa sojin Gwamnatin Syria sun kashe mutane akalla hamsin da biyar a wani harin kan mai uwa da wabin da suka kai kan garuruwa biyu inda masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Bashar al-Assad suka yi dafifi suna la’antar salon mulkin danniyar da ake masu.

‘Yan rajin kare hakkin bil Adama sun tsegunta cewar jiya lahadi an kashe mutane akalla 42 lokacin da sojin Syria cikin motocin sulke suka rika aman harsasai da sanyin safiya a kan gabashin garin Deir el-Zour.

Shugaba Bashar al-Assad ya kare matakin da sojin Gwamnatin ke dauka a kan masu zanga-zangar da cewa mataki ne na kakkabe makiya salon mulkin jama’a da neman tada tunzuri irin na ayyukan Ta’addanci, sannan suce a zuba masu ido suci gaba da tursasawa al’ummar kasa.

A tattaunawar da Bashar yayi da ministan harkokin wajen Lebanon jiya lahadi, ya jaddada cewar Syria na kan turbar komawa baki daya ga turbar salon mulkin Demokuradiyya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG