Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Hamayya Suna Zanga Zanga A Masar


Masu zanga zanga a dandalin Tahrir suke gudu daga hayaki mai sa hawaye da 'yan sandan kwantarda tarzoma suka harba.
A Masar masu zanga zanga a birane kasar masu yawa, sun kai hari kan ofisoshin kungiyar “Ya ku ‘Yan uwa musulmi”, ko Muslim Brtoherhood a turance, a yayinda ‘yan hamayya da kuma masu goyon bayan gwamnati, suka yi zanga zanga a binrin alkahira, kan wata sabuwar dokar da shugaban kasar ya kafa.
Magoya bayan shuga Morsi suke zanga zanga da kirari yayinda suke maci.
Magoya bayan shuga Morsi suke zanga zanga da kirari yayinda suke maci.

Tarzomar ta zo ne kwana daya bayan da shugaba Mohammed Morsi, ya fifita kansa daga kan ko wani bangare na mulki, tare da ayyana cewa babu wata kotu ko hukumar kasar da take da ikon ta kalubalanci duk wata shawara da ya yanke.

A cikin wani jawabi da ya yiwa magoya bayansa a fadar shugaban kasa jiya jumma’a, Mr. Morsi yace burinsa shine ganin Masar ta kasance kasa dake da kwanciyar hankali da kuma zata samu ci gaba cikin tsanaki, kuma bashi da niyyar zama mai cikakken iko kan ko wani lamari na kasar.

Dubban magoya bayan ‘yan hamayya ciki harda mai ra’ayin ‘yan baruwana Mohammed ElBradei, wanda shine tsohon shugaban hukumar hana yaduwar makaman Atomic na Majalisar Dinkin Duniya, sun hallara a dandalin Tahrir jiya jumma’a, domin zanga zanga kan shawarar da shugaban kasar ya yanke, yayinda ‘Yan Sanda suka harba bornon tsohuwa kan gungun masu zanga-zangan.
ElBaradei ya zargi shugaban kasan da cewa ya zama “sabon fir’auna” domin ya ayyana kansa a zaman shugaba mai dumbin iko.

A biranen Port Sa’id, da Isma’ila, da Alexandria, anga masu zanga zanga suna jifa da duwatsu da wasu abubuwa msu fashewa, da kuma cunna wuta kan ofishin kungiyar Muslim Bortherhood mai mulkin kasar.
XS
SM
MD
LG