Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jamhuriyar Nijar Sun Bayyana Ra'yinsu Akan Dawowar Shugaba Buhari


Dawowar Shugaba Mohammadu Buhari Daga Birnin London

'Yan Nijar, kasar dake makwaftaka da Najeriya dake da alaka da juna ta fannin addini, al'adu da harsuna sun bayyana ra'ayinsu game da dawowar Shugaba Buhari tare da gargadin 'yan Najeriya akan zaman lafiya da yiwa shugaban da kasar fatan alheri.

Duk wadanda suka yi furuci sun yiwa Allah godiya da dawowar Shugaba Buhari suna cewa dama abun da suke jira su ji ke nan tare da fatan Allah ya kara mashi lafiya.

Sun yi addu'ar Allah ya kara dankon zumunci dake tsakanin kasar Nijar da Najeriya. Suna fatan Allah ya bada hakurin zaman makwaftaka tare da sauran wasu kasashen dake makwaftaka da su.

Sun kira gwamnatin Najeriya da ta bude iyakokin kasashen biyu ayan an sa mahukumta sun gyara matsalolin da ake fuskanta domin kasuwanci ya ci gaba tsakanin kasashen biyu da ma sauran kasashen.

Wani yace Buhari ikon Allah ne, ikon Allah ne ya bashi mulki, shi ya kashi jinya shi kuma ya dawo dashi a lokacin da ya ga dama. Ya kira 'yan Najeriya da su rungumi wannan iko na Allah

Akan kasar sun ce 'yan Najeriya sun yi yaki domin kasar ta kasance daya saboda haka kada wani ya fara wani sabon yakin kuma. Su guji duk abun da zai kaiga yaki.

Tare da ikon Allha Buhari zai yi maganin tsaro nan da dan lokaci kadan. Buhari zai cimma burin abun da ya sa aka zabeshi. Injisu, Buhari ya yi aiki kuma yana aiki wa Najeriya da kasashen dake makwaftaka da ita ne su ci gaba ta yadda kasashen ba zasu dinga zuwa neman taimako a kasashen waje ba inda ake wulakantasu. Buhari na son su zauna da gindinsu, su kuma tsaya kan kafafuwansu daram dam.

Wani ya gargadi 'yan Najeriya Musulmi da Kiristoci kudu da arewa da ma wadanda basu da addini su san cewa Buhari na kowa ne, na Najeriya ne gaba dayanta. Yana mai cewa samun irin shugabancin Buhari nada wuya. Yayi fatan Allah ya bashi lafiya ya ci gaba da nuna adalci a duk lamuransa.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG