Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka Suna Yakin Neman Zabe A Jihar Ohio


Campaign The Undecided
Shugaba Barack Obama na Amurka da dan takarar jam’iyyar Republican dake kalubalantarsa a zaben bana Mitt Romney, duk zasu yi yakin neman zabe yau laraba a Jihar Ohio dake yankin tsakiyar Amurka.

Jiya talata Mr. Romney ya fara rangadin yakin neman zabe na kwanaki biyu cikin motar safa a jihar mai masana’antu, inda ya hau kan durom tare da mataimakinsa Paul Ryan a kusa da birnin Dayton. A wannan gangamin farko da dan takarar shugaban da mataimakinsa suka yi tare cikin ‘yan kwanakin nan, sun ce zasu iya farfado da tattalin arzikin Amurka, abinda suka ce Mr. Obama ya kasa.

A yau laraba, Mr. Romney zai yi wani gangami tare da shahararren dan wasan Golf, Jack Nicklaus, wanda dan asalin Jihar ta Ohio ne.

Shi kuma shugaba Obama zai nemi goyon bayan wani bangaren masu jefa kuri’a dake da muhimmanci, watau matasa, a gangamin da zai yi a wasu jami’o’i guda biyu a jihar ta Ohio a yau laraba.

Ana saura makonni shida kafin zaben na ranar 6 ga watan Nuwamba, Mr. Obama ya fara yin fintinkau ma abokin takararsa a kuri’un neman ra’ayoyin masu jefa kuri’a na Jihar Ohio da kuma sauran jihohin kasar nan.
XS
SM
MD
LG