"Shirin zuwa turai babu visa ya fara aiki, Allah Ya daukaka turai, Allah Ya daukaka Ukraine!" kamar yadda ya rubuta a shafinsa na shugaban kasa a dandalin Tweetet da safiyar jiya Lahadi.
Shirin zai baiwa dukkan 'yan kasar wadanda suke da Fassfo dauke da cikakkun bayanansu su shiga dukkan kasashe dake kungiyar tarayyar turai in banda Ingila da Ireland, na tsawon kwanaki 90 cikin ko wani wata shida, a ziyara yawon bude ido ne ko kuma na sada zumunci ga dangi ko abokan arziki.
Ranar Asabar ne Poroshenko ya gana da takwaran aikinsa na Slovak Andrej Kiska kan iyakokin kasshen biyu, a bikin bude "kofar zuwa Turai."
"Marabanku a turai," Kiska ya gayawa gungun mutanen da suka hallara. Ina kira gareku da ku ci gaba da aiwatar da sauye-sauye.
Facebook Forum