Accessibility links

Yan Libya suna zaben farko cikin shekaru 60

  • Jummai Ali

Zaben farko a kasar Libya, cikin shekaru 60

A karon farko cikin shekaru sittin, yan kasar Libya suna zaben daya kunshi jam'iyun siyasa da dama

A karon farko cikin shekaru sittin, yau asabar yan kasar Libya suke zaben daya kunshi jam’iyun siyasa da dama.

Wadanda suka cancanci yin zabe, zasu zabi wakilan Majalisar wakilai ta wucin gadi mai kujeru maitan. Majalisar ce zata kafa gwamnatin wucin gadi ta tsara daftarin tsarin mulki kafin ayi zaben Majalisar wakilai badi idan Allah ya kaimu.

Jami’an tsaro suna gadin rumfunan zabe a zaman shirin kota kwana, domin rigakafin yiwuwar barkewar tarzoma.

Jami’an Libya sunce wasu masu zanga zanga sun dagula zabe a wasu rumfunan zabe a gabashin kasar ciki harda biranen Benghazi da Ajdabiya. Wasu kungiyoyi kuma a gabashin kasar, sunyi ikirarin cewa jami’ai a baban birnin kasar sunyi watsi da yankin, kuma suna bukatar a basu karin iko.

Ana dai yin wannan zabe ne kasa da shekara daya bayan da tsohon shugaban kasar, marigayi Moammar Gaddafi ya mutu bayan da mayakan dake hamaiya da gwamnati sun kama shi.

Wasu masu zabe sunje rumfunan zabe, sun rufe jikinsu da sabuwar turar Libya mai launin ja da korai da kuma baki.

Fiye da jam’iyun siyasa dari da arba’in ne suke takara. Masu nazarin harkokin siyasar kasar sunyi hasashen cewa, masu ra’ayin ka’idodin addinin Musulunci zasu samu nasara.

A wata tarzoma data auku jiya juma’a, wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, sun bude wuta akan jirgin sama mai saukar angulu dake jigilar kayayyakin zabe suka kashe wani jami’in zabe a cikin jirgin. Kusa da birnin Benghazi aka kai harin, kuma ba’a tantance dalilin ke wannan hari ba .

XS
SM
MD
LG