Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisa Kan Katin Zabe


Ginin majalisun tarayyar Najeriya.
Ginin majalisun tarayyar Najeriya.

Dan majalisar wakilai Ibrahim Bello Rigachukun ya bayyana dalinsu na tsayar da dokar bada katin zabe na wucin gadi

A firar da yayi da wakilin Muryar Amurka Onarebul Ibrahim Bello ya bayyana dalilan da suka sa suka kafa dokar bada katin zabe na wucin gadi ga wadanda suke gudun hijira ko wata matsala ta rabasu da gidajensu.

Majalisa tana so ta baiwa mutane da suka afka cikin wani bala'i kamar na jihohin Borno, Adamawa da Yobe da yanzu suke sansanonin 'yan gudun hijira su samu damar kada nasu kuri'un. Daga bisani kuma idan sun koma gidajensu sai a basu katin zabe na dindindin. Wajibi ne a bisu inda suke su samu su jefa kuri'a.

Akan wai lokaci ya kure domin kafin shugaban kasa ya sa hannu a dokar lokacin zaben yayi sai dan majalisar yace su dai sun yi nasu aikin sauran kuma ya rage ga shugaban kasa.

Wadanda suke gudun hijira sun gwammace gwamnati ta taimaka masu su koma gidajensu ba zabe ya damesu ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG