Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dattawa Sun Ziyarci Yola Su Ga Nasarorin da Aka Samu Kan Boko Haram


Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Wannan ziyara karkashin Sanata Ali Ndime ita ce ta uku da wakilan majalisar zasu ziyarci Borno da nufin ganin nasarorin da aka samu kan 'yan Boko Haram

Yayin ziyarar 'yan majalisar sun je asibitn gwamnatin tarayya dake Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Wani abu kuma da ya kai 'yan majalisar shi ne ganin wadanda rikicin ya rutsa dasu sabili da haka suka nufi asibitin gwamnatin tarayya dake birnin Yola. 'Yan majalisar, ganin yadda asibitin ke aiki sun ce zasu tabbatar an daga darajar asibitin zuwa na koyaswa.

A jawabinsa shugaban asibitin Farfasa Awal Abubakar ya bayyana irin kokarin da sukeyi na taimakawa har ma sun kafa wata gidauniya saboda wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. A cewarsa kwalliya tana biyan kudin sabulu.

Duk wadanda suke zuwa asibitin sanadiyar rikicin Boko Haram Farfsa Abubakar yace suna basu magani idan kuma ta kama a yi masu aiki ana yi mas ba tare da karbar ko kwandala ba daga garesu.

Asibitin ya samu taimako daga NEMA da gwamnatin jiha da International Rescue da kuma Victims Support Fund.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

XS
SM
MD
LG