Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dattawan Amurka Sun Bukaci Shugaban Kasa Ya Fayyace Masu Matsayin Dakarunsu a Kasar Nijar


Hafsan hafsoshin Amurka da Sanata John McCain, a tsakiya, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawan Amurka
Hafsan hafsoshin Amurka da Sanata John McCain, a tsakiya, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawan Amurka

Bayan da 'yan ta'ada suka kashe sojojin Amurka hudu a wani kwantan bauna da suka yi a Jamhuriyar Nijar, 'yan majalisar dattawan kasar ta Amurka sun bukaci shugaban kasa ya fayyace masu matsayin sojojinsu a kasar ta Nijar

Jiya Lahadi wasu fitattun 'yan Majalisar Dattawan Amurka sun yi kira ga fadar Shugaban Amurka ta White House da ta fito fili ta fayyace matsayin zaman mayakan Amurka a Janhuriyar Nijar bayankashe sojojin Amurka hudu da aka yi, a wani kwantan bauna da aka masu a farkon wannan watan.

A wasu hirarrakin da aka yi da su a lokuta dabam dabam a shirin gidan talabijin na NBC mai suna, "Meet the Press," Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican da kuma Shugaban 'yan Democrat marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sen. Charles Schumer sun ce su na goyon bayan yunkurin da Sanata John McCain ya yi a makon jiya na neman cikakken bayani game da wannan harin da kuma matsayin Amurka a yaki da ISIS a wannan kasa ta Yammacin Afirka. Da Graham da Schumer sun ce ba su san akwai sojojin AMurka da dama a Nijar ba.

Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis ya gaya ma Graham da McCain, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Soji a makon jiya cewa rundunar sojin Amurka na dada karkata yakin da ta ke yi da ta'addanci zuwa Afirka.

Jami'an Amurka na ganin wata kungiyar ta'adda a yankin, wadda kuma ta ke da alaka da ISIS, ita ce ta kai harin na Nijar. To amma har yanzu hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon na binciken yadda al'amarin ya faru.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG