Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Nijar Sun Musanta Zargin Kara Wa Kansu Kudaden Alawus-Alawus


Majalissar dokokin jamhuriyar Nijer.
Majalissar dokokin jamhuriyar Nijer.

Majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ta karyata wasu bayanai da ke cewa ‘yan majalisar sun fara yunkurin kara wa kansu kudaden alawus-alawus duk da yanayin talauci da tsadar rayuwar da al’umma ke fuskanta, kuma a lokacin da matsalar tsaro ta addabi dubban ‘yan kasar a sassa da dama.

Tun a tsakiyar watan Nuwamban 2022 ne dambarwa akan yunkurin kara wa ‘yan majalisar dokokin kasar Nijar kudaden alawus-alawus ta kunno kai. Yayin da wasu ke ganin dacewar matakin a bisa dalilai na inganta yanayin rayuwar wakilan al’umma wasu kuwa na nuna rashin amincewarsu da abinda suke kira hanyar kara wa kasa larura a wani lokaci da ake cikin mawuyacin hali, wannan ne dalilin da ya sa majalisar ta yi zama a ranar Laraba domin fayyace sassan da ta yi wa gyaran fuska a dokar biyan kudaden alawus din ‘yan majalisa, kamar yadda Honorable Kalla Moutari, shugaban kwamitin ‘yan majalisa mai kula da sha’anin doka ya bayyana.

Ta hanyar wannan zama majalisar na kokarin wanke kanta daga zargin da take fuskanta, dalilin da ya sa ra’ayoyi suka zo daya a tsakanin ‘yan majalisar masu rinjaye da na adawa game da wannan magana ta gyaran fuskar dokar kudaden alawus.

Aikin dan majalisa wani abu ne da ya ta’allaka kan maganar kare hakkokin jama’ar kasa, sanin muhimmancin wannan matsayin ne ya sa ‘yan majalisar dokokin Nijar ke da mafi karancin albashi idan aka kwatanta da takwarorin aikinsu na kasashen yammacin Afrika, inji Honorable Boukari Sani Zilly.

Sabon tsarin biyan kudaden alawus-alawus din da aka yi mahawara a kansa ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba ya sami amincewar dukkan ‘yan majalisa 151 da suka halarci zauren majalisar kafin a nan gaba a gabatar wa bangaren zartarwa kudirin don tabbatar da shi a matsayin doka ko kuma a maido da shi don sake yi masa karatu na biyu.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00
XS
SM
MD
LG